Uncategorized

HARSHENKA ŸANCINKA

Koyo da koyarwa cikin harshen uwa, ingantacciyar hanya ce “sambeɗar” zuwa mafita daga jahilci da matsanancin talauci da rashin aikin yi da ke addabar al’umar mu ta Hausawa, musamman matasa. Babu al’umar da ta yi fice a duniya wajen cigaban tattalin arzikin zamaninta, ba tare da ta rungumi yin amfani da harshenta cikin lamuran koyon ilimin zamaninta ba.

Babu laifi a koyar da yaro wani baƙon harshe, kamar Turanci ko Faransanci, a matsayin darasi mai zaman kansa. Amma kuskure ne a tursasa shi ya koyi sauran darussa cikin harshen da ba nasa ba, koda kuwa wannan baƙon harshen shi ya fi kowanne harshe karbuwa a faɗin duniya.

Abin mamakin ma shi ne, da muke yaudarar kawunan mu wajen koyar da yaro sabon ilimi cikin wani baƙon harshen cikin lokaci guda. Haba jamma’a ? Ai garajen ya yi yawa ! Kamar yadda masu iya magana suka ce, an cewa sarkin garaje, “ga dami” sai ya wuf ya ce “a saka masa miya” 🤣

Tun daga nan aka ɗauki hanyar ruɗar ƙwaƙwalen mu tun daga farkon yarintar mu. Ina ma laifin a fara koyar da shi ilimin da ake son koyarwa cikin harshen mu na uwa, wanda shi ya muka ƙwarewa, shi kuma wancan turancin “alabasshi”, a koyar da mu a cikin wani aji mai zaman kansa ?

Kuma bincike ya nuna cewa da can hakan a ke yi, a farkon zuwan boko ƙasar Hausa, lokacin da Hans Vischer ( Ɗan Hausa), ya kafa makarantar Gidan Ɗan Hausa a Kano. Masana sun tabbatar da wancan tsarin ya fi na yanzu inganci, kamar yadda shahararren marubucin nan, Hamisu Isa Sharifai, ya gabatar cikin ƙasidarsa mai suna GWAGWARMAYAR DA TA KE GABAN HAUSAWA A KARNI NA 21. Shi ma binciken da Farfesa Aliu Babs Fafunwa ya shafe shekaru takwas yana yi mai suna “Education in Morher Tongue: The Ife Primary Education Research Project”, wanda ya gudanar daga 1970 zuwa 1978, ya ƙara tabbatar da cewa wannan lamari haka yake.

Wannan batu kuwa kullum yana ƙara bayyana cikin azuzuwan da muke horon ɗalubai a EngausaHub.com . Domin a nan ne muka samar da wani yanayi mai abin mamaki, da ke fito da baiwar waɗanda basu sami zarafin shiga makarantun boko ba, balle su ji Turanci. Sai ka ga almajiri daga tsangaya ya fi injiniyan da ya fito daga jami’a saurin fahimtar dabarun fasahar zamani, saboda an fassara masa ilimin zuwa harshe sa na Hausa. Sai muka gane cewa, ashe wancan da ya fito daga Jami’a ba basira ya fi wannan almajirin ba, turanci kawai ya fi shi fahimta, da aka zare Turancin sai baiwar wancan almajirin ta bayyana a fili.

To ashe dai akwai wani shinge da ya tokare hanyar fito da baiwar da ke cikin ƙwaƙwalen matasan mu har ma da ta yara ƙanana. Wannan kuma ba wani shinge bane face na harshen Turancin da a ka ƙaƙaba mana shi a tun daga matakin farko na koyon karatun zamani. Babu laifi a sako Turanci a matsayin darasi mai zaman kansa, wanda dalubai zasu koyi amfani da harshen tunda shi ne harshe mafi kabuwa a duniya, musamman a bangaren kimiyya da fasaha.

Akan ruɗi ƙwaƙwalen wasu ÿan Nigeria cewa idan kowanne bangare na ƙasar ya yi riƙo da harshen da ya fi shahara cikin al’umar sa, to da wanne harshe za mu yi magana idan aiki ya haɗa mu da abokan zaman mu Yarabawa ko Ibo ? Wannan ai ba wani baƙon abu bane a duniyar harsuna. Shi kenan sai mu riƙi harsuna guda hudu na gudanar da aikin ofis, wato Hausa da Yarabanci da Inyamuranci da Turanci. Kowanne bangare na Nigeria ya riƙi harsuna guda biyu, kamar a arewa sai mu riƙi Hausa da Turanci, a kudu-maso yamma su riƙi Yarabanci da Turanci, kudu-maso gabas kuwa sai su riƙi Ibo (Inyamuranci) da Turanci. Akwai ƙasashe a duniya da ke riƙar harsuna sama da guda ɗaya a matsayin harsunan gudanar da mulki, irin su Finland 🇫🇮 da ke amfani da Finnish da Swedish, Canada 🇨🇦 na amfani da English da French.

Watakil mai tambaya ya ce, ai duk waɗancan ba ƙasashen Africa bane, sai na ce masa ya bincika zai ga a South Africa harsuna daban-daban har guda 12 ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan ofis. Egypt 🇪🇬 kuwa Larabci ne nasu, kuma sun tabbatar shine yafi anfanar su wajen koyo da koyarwa na dukkan darussa har kimiyya da fasahar. Haka kuma ƙasar Sudan 🇸🇩, Larabci ne da Turanci a haɗe.

Idan ka koma Asiya zaka tarar da misalai masu yawan gaske. Misali na kukusa shine na ƙasar Malasia, wacce amfani da harshen uwa shine tushen cigaban fannin ilimin su da haɓakar tattalin arzikin su. Sun riƙi harshensu na Malay (Bahasa Malaysia) da kuma Turanci (English), domin tabbatar da fahimtar ilimin zamani da amfani da shi yadda ya dace.

Dukkan wannan Ƙasashe da na ambato a sama sun yi wa Nigeria 🇳🇬 fintinkau wajen haɓakar ilimin zamani, saboda sun karɓowa kawunan su ŸANCIN HARSHE (Linguistis Human Right). Mukuwa da ba mu fahimci wannan ÿancin ba, balle mu miƙa hannu mu karɓo shi, sai muke ta yin tururuwa wajen fita ƙasashensu don neman ilimin boko, amma har yanzu babu wani cigaban ilimi da muka samo daga can, sai ma cibaya da namu harkokin ke yi, irin na mai haƙar rijiya. Kamar dai misalin “mai ganin hadari ne da ke wanka da kashi”. Sai mu kwashi dukiya mai yawa ta al’umma, mu tura mutane can, idan suka dawo sai su tarar babu yanayin da zai basu damar amfani da shi yadda ya kamata a nsn, kafin wasu shekaru sai ilim nasu ya tsufa ko ya tashi ya koma gidan jiya, su kuwa su “koma ruwa tsundum”.

Fahimtar wannan hikimar da baiwar da ke ƙunshe cikin harshen uwa, zai sa mu ƙara fahimtar sakon da ayar Al’ƙur’ani mai girma take isarwa a gare mu, inda Allah Maɗaukakin Sarki Yake cewa:

“Ya ku mutane! Lalle ne Mu, Mun halicce ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da ƙabilu, domin ku san juna. Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, (shi ne) wanda yake mafificinku a taƙawa. Lalle ne Allah Masani ne, Mai kididdigewa” [Qur’an 49:13]

Iya Musa

Content Creation: Crafting engaging and informative written pieces for blogs. Social Media Management: Building and managing a brand presence across social media platforms, keeping audiences engaged.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button