Littafi mai suna “Ba Afkin Kwalin Digiri ba, a Sami Ƙwarewa” ya Iso ENGAUSA HUB
Ƙafa-da-ƙafa, Saƙon Prof. Shk. Isa Ali Ibrahim Pantami ya ƙaraso Engausa Global Tech Hub ta hanyar Engr. Ibrahim Yakubu (mataimaki na musamman), Sham’un A. Damji, da Ishaƙ Ali da Nurul-Amin Mustapha (ma’aikatan NITDA).
Maisuga Library da ke cikin cibiyar ta EngausaHub.com ta gwangwaje da shahararrun littattafan nan da bujimin malamin ya rubuta, wato SKILLS: RATHER THAN JUST DEGREES da kuma CYBERSECURITY: INITIATIVES FOR SECURING A COUNTRY. Allah Ya ji ƙan mahaifan malam, Ya ƙaro albarka mai yalwa cikin rayuwar sa, Ya sa dukkan matasan mu su amfani wannan baiwa da Allah Ya yi masa 🤲
Da na afka wa littafin da ya fi ɗaukar hankali na da karatu, wato “Ba Afkin Kwalin Digiri ba, a Sami Ƙwarewa” ( SKILLS: RATHER THAN JUST DEGREES), babu abin da ya mamaye tunani na sai tausayin matashin da bai sami zarafin karanta wannan littafi ba, ko kuma samun irin bayanan da ya ƙunsa daga sauran kafofin sadarwa.
Kafin samun damar fassarar wannan littafi, IN SHÃ ALLAHU zan yi iyakar bakin ƙoƙari wajen isar da mafiyawancin saƙonnin da ke cikin wannan littafi domin amfanin al’umar mu da kuma zaburar da matasan mu kan abin da duniya ke tafiya a kai a yanzu, musamman kan TATTALIN ARZIƘIN FASAHAR ZAMANI (samun ƙwarewa cikin fannin, da anfani da ƙwarewar wajen samar da aikin yi ga matasa da haɓakar arziƙin al’umma bakiɗaya).
Tuni a ka gina tsare-tsaren koyarwar cibiyar ENGAUSA HUB kan gwadabe mai kama da abin da wannan muhimmin littafi ya ƙunsa. Wannan kuwa ya samo asali ne daga irin bincike-binciken hanyoyin samun mafita daga halin da muka sami kan mu na rashin aikin yi na matasa da lalacewar tarbiya da wanzuwar talauci “mai naci” da rashin zaman lafiya.
Hukumar NITDA Nigeria mai alhakin BUNƘASA FASAHOHIN ZAMANI wacce jajirtaccen shugaban ta, Mal. Kashifu Inuwa Abdullahi ke shugabanta a yanzu, ta taimaka ƙwarai da gaske wajen saita sahun ENGAUSA HUB da sauran cibiyoyi da makarantu da hukumomi cikin faɗin Najeriya, kan wannan ingantacciyar turbar cigaba mai ɗorewa. Duka cikin tagomashin hikimomi da Allah Ya kimsa wa wannan bawa Nasa, abin koyi ga dukkan matasan wannan zamani, wato Professor Isa Ali Pantami.
ALHAMDU LILLAH