Ga wasu muhimman jawabai kan samun nasarar fara karatu cikin ENGAUSA ONLINE ACADEMY a kyauta
Ga wasu muhimman jawabai kan samun nasarar fara karatu cikin ENGAUSA ONLINE ACADEMY a kyauta, har zuwa sati mai zuwa IN SHÃ ALLAH.
1. Duk wanda bai ga saƙo a Gmail ɗin da ya cike form ba to dayan biyu ne, ko dai bai kai 24hrs da cikewa ba, ko kuma ba daidai ya rubuto Gmail address ɗinsa ba.
2. Wanda kuma ya ga an turo masa saƙo a Gmail ɗinsa ko SMS ba, kuma ya danna link ɗin da aka turo masa, har ya yi ƙoƙarin logging in, amma ya ƙi kai shi cikin ENGAUSA ONLY ACADEMY, to shima ɗayan biyu ne; kodai ba shine Gmail ɗin da ke kan wayar hannunsa ta Android ba, ko kuma ba daidai yake saka password ɗinsa ba. Idan ya manta password ɗin ne kuwa, to sai ya yi resetting password ɗin.
3. Wasu ma Home Address suka saka a maimakon Gmail Address. Wannan kuwa babu yadda muka iya dasu, sai sun fara samun wanda zai fara dora su a kan hanyar ilimin fasahar zamani daga tushe cikin makusantansu, ko kuma su zo ENGAUSA HUB domin shiga aji, a koyar dasu dalla-dalla.
Duk mai neman karin bayani sai ya tuntuɓe mu a kan wannan lambar wayar: 07038224643
ALLAH YA SA MU DACE