SkillsUncategorized

BA NAKASASSHE SAI KASASSHE

BA NAKASASSHE SAI KASASSHE 💪

Cikin wannan rana da a ke bikin RANAR MATASA TA DUNIYA (International Youth Day 2023) mun karɓi baƙuncin shuwagabannin ƘUNGIYAR MASU LARURAR LAKA, Spinal Cord Injuries Association of Nigeria (SCIAN), domin tattauna buƙatar haɗin gwiwa tsakanin ta da ENGAUSA FOUNDATION FOR INCLUSIVE SKILL ACQUISITION (EFSIA), wanda EngausaHub.com ta samar. Mun tattauna kan hanyoyin da za mu bi domin sauƙaƙawa ÿaÿan wannan ƙungiya samun zarafin koyon sana’oin hannu domin dogaro da kawunan su, kamar kowa. Samar da wannan hanyoyi zai taimaka wajen yanke uzurin duk wani mai yin bara saboda wata larura da bata hana yayi amfani da wata lafiyayyiyiyar gaba a jikin sa ba.

Cikin tattaunawar da muka yi, mun tuno da babban abin koyo ga Hausawa masu larurar laka, wato baban mu, Dr. Habibu Sani Babura, wanda shine ake yi wa lakabi da “Uban marar uba”, ko “Ba nakasasshe sai kasasshe, ko “There is ability in disability”. Wato ba shine ya ke neman taimako daga gurin jama’a ba, jama’ar ne ke neman taimakon sa, tsawon shekaru masu yawa da ya shafe a kan kujerar da a ke tura shi, cikin Bayero University Kano (BUK). Domin kuwa masu turashin ma a karkashin inuwar sa suke karatu a jami’a, har ma da samun aiki bayan kammala jami’ar. Kuma abubuwan da suka sanya rayuwar sa ta yi albarka yana cikin wannan larura, sun hada da ilimi mai anfani da ya tara, sai hakuri da tawakkali da son taimakon al’umar da ke tururuwa zuwa gidan sa da ofishin sa, daga sassan duniya.

ENGAUSA HUB ta samar da sabbin hanyoyin koyar da duk wani nau’in da jinsi na mutane, matukar suna da isasshen hankalin da za su koyi sana’oin dogaro da kai na fasahohin zamani. Wannan tsarin shi ake kira da “inclusive system of education” kamar yadda SUSTAINABLE DEVELOPMENT GOAL NO.4 (Quality education for all) ya tanada.

Chairman ɗin wannan ƙungiya, Abdurrahman Uba Daushe, ya yi tsokaci mai amfani kan yadda iyaye za su kula da irin gaɓobin da za su doka wajen horon yaran su. Kamar yadda ya yi kira da a guji yin “dundu” a bayan yaro, ko wani duka da zai iya lahanta masa laka. Ya kuma yi tsokaci kan buƙatar wayar da kan al’umma kan yadda za’a kula da wanda ya haɗu da jarrabawar larurar lakar; domin guje wa wasu matsalolin da ka iya ta’azzara halin da ya sami kansa, idan ba’a san da su ba.

ENGAUSA FOUDATION ta yi maraba da dukkanin bukatun haɗin gwiwar da wannan kungiya ta gabatar a rubuce. Kuma ta bayar da scholarship ga ÿaÿan wannan kungiya ta SCIAN, daga cikin ajin da ke gudana a yanzu. Sannan ta ƙara da tagomashin ragin kashi hamsin bisa ɗari na registration ɗin masu wannan larura, a sauran azuzuwan da za’a buɗe nan gaba IN SHÃ ALLAHU.

 

Iya Musa

Content Creation: Crafting engaging and informative written pieces for blogs. Social Media Management: Building and managing a brand presence across social media platforms, keeping audiences engaged.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button