GYARAN KWANFIYUTA: MADOGARAR KAMA SANA’AR ZAMANI GA MATASA
Wannan shi ne sabon ajin da a ka ƙaro a cikin azuzuwan Engausa Global Tech Hub, domin KOYON GYARAN KWANFIYUTA.
GYARAN KWAMFIYUTA wata sana’a ce mai tarun alkhairi, domin mai kwarewa a wannan fanni zai iya rikidewa ya zama mai tarun sana’oin zamani kala-kala. Ni Mustapha Habu Ringim, na sami damar budar ido cikin sana’oin fasahar zamani ne ta hanyar wannan sana’ar tun shekarar 2004 a Shy Shoping Plaza. Haka kuma na cigaba da yin ta cikin jama’ar BUK lokacin da ina dalubta, tun 2004 zuwa 2010 ALHAMDU LILLAH.
Cikin tarihin shugaban NITDA, Mal. Kashifu Inuwa Abdullahi, shima ya fara sana’oin fasahar zamani ne a tasowar sa cikin garin Hadejia da Dutse da Kano. Kuma har yanzu ya alfahari da wannan tarihin nasa abin koyi ga matasan wannan zamani.
Kamar yadda Kashifu ya fada lokacin taron yaye daluban ENGAUSA HUB a shekarar 2022: “Mu ba mu sami irin wannan damarmakin ba a wancan lokacin, to mai zai hana matasan yanzu su yi kokari su wuce nasarorin na muka samu a rayuwar mu ?”.
Allah Ya sa mu dace