Engausa Global Tech Hub ta karɓi baƙuncin Shehin Malamin mu na Jami’ar BUK, wato Prof. Aliyu Jibiya
Engausa Global Tech Hub ta karɓi baƙuncin Shehin Malamin mu na Jami’ar BUK, wato Prof. Aliyu Jibiya
A yau Engausa Global Tech Hub ta karɓi baƙuncin Shehin Malamin mu na Jami’ar BUK, wato Prof. Aliyu Jibiya. Malami mai son cigaban al’ummah. Yana daga cikin dattijan arewa da ke ƙara min ƙarfin gwiwa matuƙa gaya. Ya kan ce “Mustapha ko da wasa kada ka sake wani dalili ya sa ka sauka daga kan wannan sabuwar turbar ta ENGAUSA HUB, domin tana rufe wani ƙaton gurbi ne da muka daɗe muna neman hanyar rufe shi”.Shi kuwa shehin malamin mu, Prof. Mansur Sokoto cewa yayi “ENGAUSA HUB wata ƙofa ce da tsawon lokaci muka daɗe muna laluban ta a cikin duhu, sai Allah Ya baku ikon gano inda take, kuma Ya baku ikon buɗe ta”.Prof. Hafizu Miko Yakasai kuwa, bayan ya yi bayanai irin na sauran takwarorin sa, sai ya ƙara da cewa, ya sadaukar mana da lokutan sa da ilimin sa, duk inda ake neman gudunmawar sa kan cigaban wannan tafiya, ko a ƙurarren lokaci ne, kada mu yi ƙasa a gwiwa wajen gayyatar sa.Manyan malaman jami’oi, irin su Prof. Ajiya, Prof. S. S. Adamu, Prof. Ahmad Baita, da Dr. Binta Usman da Dr. Muhammad Buhari da Dr. Bature Amir, Dr. Abubakar Uba, Dr. Abba Lawan ba za mu manta da gudummawar su cikin wannan tafiya ba.Wannan ɓangare daya kawai na taɓo na shehunan malamai. Akwai attajirai da ÿan Nigeria mazauna turai, da iyaye mata dattijai da wasu ma da ban san su a fuska ba, sai dai a waya; da ke ƙara mana ƙarfin gwiwa da kuma taya mu da addua.Dukkan masu ƙarfafa mana gwiwa, waɗanda muka sani da waɗanda bamu sani ba, Allah Ya saka masu da Alkhairi Allah Ya sa mu dace, duniya da lahira.